Terra Industries Ta Kaddamar da Sabbin Kayan Tsaro na Zamani da Aka Kera a Najeriya
Kamfanin fasahar tsaro na Najeriya, Terra Industries, ya kaddamar da wasu sabbin kayayyakin tsaro na zamani da aka ƙera a cikin gida, a wani baje koli da aka gudanar a Abuja.
Kayayyakin da aka nuna sun haɗa da jiragen yaƙi marasa matuƙa masu hana hare-haren sama (interceptor drones), motocin gano da kawar da nakiyoyi ba tare da direba ba, da kuma manhajojin tattara bayanan sirri na yaƙi ta amfani da fasahar zamani.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an soja da wakilan gwamnati, lamarin da ke nuna ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin fasaha masu zaman kansu da rundunar sojin Najeriya wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa sabbin kayayyakin an ƙera su ne domin inganta tattara bayanan sirri a fagen daga, gano da kawar da abubuwan fashewa, da kuma ƙarfafa saurin mayar da martani a yaƙi da ta’addanci da matsalolin ‘yan bindiga.
Wannan mataki na Terra Industries na nuna sauyawa daga ayyukan tsaron gine-gine da masana’antu zuwa shiga kai tsaye cikin samar da fasahar soji, wanda masana ke ganin zai taimaka wajen ƙarfafa dogaro da kai na Najeriya a harkar tsaro tare da rage dogaro da kayan yaƙi daga ƙasashen waje.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0