Babu Namijin da Zai Iya Gamsar da Mace Gaba Ɗaya – Fasto Funke Adejumo
Babu Namijin da Zai Iya Gamsar da Mace Gaba Ɗaya – Fasto Funke Adejumo Ta Shawarci Mazajen Aure
Shahararriyar malamar addinin Kirista kuma wacce ta kafa Agape Christian Ministries, Funke Adejumo, ta shawarci mazajen aure da kada su wahalar da kansu wajen ƙoƙarin faranta wa matansu rai fiye da kima, tana mai cewa babu wani namiji da zai iya gamsar da mace gaba ɗaya.
A cikin wani faifan bidiyon wa'azi da ya bazu a kafafen sada zumunta, Fasto Adejumo ta ce tana magana ne daga matsayinta na mace, inda ta jaddada cewa neman gamsar da mace gaba ɗaya abu ne da ba zai yiwu ba.
Ta ce, "Ina gaya wa duk mazajen aure, kada ku kashe kanku kuna ƙoƙarin faranta wa mace rai. Ni mace ce nake gaya muku, kuma babu wanda zai iya gamsar da mace gaba ɗaya."
Malamar ta ci gaba da misalta hakan da yadda mutane ke sauya wasu halittun da Allah Ya ba su, inda ta ce Allah Ya ba mutane farce da gashin kai na asali, amma da yawa suna maye gurbinsu da na roba ko kuma gashin ƙarya (wig). A cewarta, idan har mutum ba ya gamsuwa da abin da Allah Ya halitta masa, to bai kamata namiji ya ɗauka cewa zai iya cika dukkan buƙatun mace ba.
Sai dai duk da wannan furuci, Fasto Adejumo ta buƙaci mazajen aure da su ci gaba da nuna ƙauna, kulawa da girmamawa ga matansu. Ta bayyana cewa manufarta ita ce ta tunatar da ma'aurata cewa rayuwar aure ba ta ta'allaka ne kan neman cikakkiyar gamsuwa ba, illa dai fahimtar juna, haƙuri da kuma ci gaba da ƙoƙarin kyautata zamantakewa.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
1
Funny
1
Angry
0
Sad
0
Wow
1