FIFA Ta Amince da Sabbin Dokoki Domin Rage Bata Lokaci a Gasar Kofin Duniya ta 2026

Mar 20, 2026 - 20:35
Mar 21, 2026 - 08:11
 0  3
FIFA Ta Amince da Sabbin Dokoki Domin Rage Bata Lokaci a Gasar Kofin Duniya ta 2026

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta amince da wasu sabbin dokoki da za a fara amfani da su a Gasar Kofin Duniya ta 2026, domin rage bata lokaci da kuma inganta sahihancin yanke hukunci a wasa.

Rahotanni daga ESPN sun bayyana cewa, sabbin dokokin sun kunshi muhimman sauye-sauye da ake sa ran za su kawo gyara a yadda ake gudanar da wasanni.

Daga cikin sabbin dokokin akwai:

Dole ne dan wasan da aka sauya ya bar fili cikin dakika 10 kacal. Idan bai yi haka ba, wanda zai maye gurbinsa zai jira minti 1 kafin ya shiga filin wasa.

Ana bukatar a yi jefa kwallo (throw-in) cikin dakika 5, in ba haka ba za a bai wa abokan hamayya kwallon.

Duk dan wasan da aka yi masa jinya a fili, dole ne ya fita na tsawon minti 1 kafin ya dawo wasa.

An kuma bai wa tsarin VAR damar duba katin gargadi na biyu (second yellow card) da kuma hukuncin bugun kusurwa (corner kick) idan akwai kuskure bayyananne.

Masana kwallon kafa na ganin cewa wadannan sauye-sauye za su taimaka wajen rage jan lokaci da kuma kara gaskiya a hukunci, musamman a manyan gasa irin su Kofin Duniya.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan ko wadannan dokoki za su kawo sauyi mai kyau ko kuma su kara rikitar da wasan.

Shin wadannan sabbin dokoki za su inganta kwallon kafa ko akasin haka?

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0