Sabon Kudiri: Tinubu Ya Nemi Garambawul ga Dokokin Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuka

Jul 9, 2026 - 16:51
 0  1
Sabon Kudiri: Tinubu Ya Nemi Garambawul ga Dokokin Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuka

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wa Majalisar Dattawa da wani kudirin doka da ke neman sake fasalin tsarin gudanar da shari’ar manyan laifuka a Najeriya domin inganta saurin yanke hukunci da kuma ƙarfafa adalci a ƙasar.

Kudirin ya tanadi soke Dokar Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuka ta shekarar 2015 tare da samar da sabuwar Dokar Gudanar da Shari’ar Manyan Laifuka ta shekarar 2026. A cewar shugaban ƙasar, sabon kudirin zai taimaka wajen daidaita tsarin shari’a da kuma kawar da matsalolin da suka dade suna haddasa tsaiko wajen sauraron kararraki.

Tinubu ya bayyana cewa akwai bukatar sabunta dokokin da ke tafiyar da shari’o’in manyan laifuka domin su dace da sauye-sauyen zamani da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da shari’a cikin gaskiya, inganci da sauri. Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta fara nazari kan kudirin nan ba da jimawa ba domin yanke hukunci a kansa.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0