Tsohon IGP Adamu Ya Shiga Takarar Gwamna a Nasarawa, Ya Mika Fom ga Al-Makura
Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu, ya sayi fom ɗin takarar gwamna a Jihar Nasarawa karkashin jam’iyyar APC, lamarin da ke ƙara ɗumama siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa Adamu ya mika fom ɗin nasa ga tsohon gwamnan jihar, Tanko Almakura, wanda ake ganin na daga cikin manyan jiga-jigan APC a yankin. Wannan mataki na nuni da neman goyon baya daga manyan ‘yan siyasa domin ƙarfafa matsayinsa a fafatawar dake tafe.
Ana sa ran Adamu zai fafata ne a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da Sanata Wadada, wanda ke samun goyon bayan gwamnan jihar na yanzu, Engr Abdullahi Suke.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa wannan takara za ta kasance mai zafi, duba da irin ƙarfin da kowanne ɓangare ke da shi a cikin jam’iyyar. Yayin da Adamu ke da kwarewa a harkar tsaro da kuma goyon bayan wasu jiga-jigai, Sanata Wadada na cin gajiyar kusanci da gwamnatin jihar.
Ana sa ran wannan fafatawa za ta ƙara fito da tasirin siyasa da kuma gwada karfin ‘yan takara a cikin APC, yayin da al’ummar Jihar Nasarawa ke jiran ganin wanda zai zama zakaran jam’iyyar kafin babban zaɓe.
Za a ci gaba da bibiyar wannan lamari domin kawo muku sabbin bayanai kan yadda siyasar jihar ke ƙara ɗaukar zafi.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0