Dan Takaran Kujeran Gwamnan Jahar Gombe Ajam'iyar PDP Farfesa Pantami Ya Nuna Damuwarsa Kan Matsalar Tsaro Da Hare-Haren Makarantu Da Al’ummomi A Najeriya
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, CON, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na Najeriya, musamman sakamakon yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane, hare-hare kan al’ummomi, da kuma abin da ya bayyana a matsayin abin takaici na kai hare-hare kan makarantu da yara marasa laifi.
A Jihar Kogi, rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’adda sun kai hari garin Ayegunle Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu, inda suka kashe wani mazaunin yankin, suka jikkata wasu tare da yin garkuwa da mutane sama da goma sha biyar, ciki har da fasinjojin wata motar haya. Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalar tsaro a jihar, bayan wasu hare-hare makamantan wannan da suka ƙara jefa mazauna yankin cikin fargaba.
A Jihar Plateau kuwa, wasu mahara dauke da makamai sun kai hari kauyen Gwon-Ajang da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi yayin wani bikin murnar zagayowar ranar haihuwa, inda suka kashe akalla mutane takwas tare da jikkata wasu goma. Wannan sabon hari ya ƙara shiga jerin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankunan Barkin Ladi, Bassa, Riyom da sauran al’ummomi a cikin watannin baya-bayan nan, lamarin da ya bar iyalai da dama cikin alhini tare da raba wasu da matsugunansu.
Haka kuma, hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin ilimi na ci gaba da tayar da hankali. A Jihar Oyo, wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare a makarantu da ke Ahoro-Esinele a Ƙaramar Hukumar Oriire, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai da dama, yayin da aka ruwaito cewa an kashe wani malami. Lamarin ya tilasta rufe wasu makarantu a al’ummomin da ke makwabtaka domin kariya.
Hakazalika, a Jihar Borno, wasu masu tayar da ƙayar baya dauke da makamai sun kai hari makarantu a al’ummar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba, inda suka yi garkuwa da yara da dama, mafi yawansu ɗaliban makarantun firamare da na yara ƙanana masu shekaru tsakanin biyu zuwa shida. Iyaye sun kalli yadda aka tafi da yaransu cikin rashin ƙarfi, abin da ya sake nuna irin raunin da makarantu da wuraren koyo ke fuskanta a yankunan da rikici ya shafa.
Pantami ya bayyana cewa waɗannan hare-hare na nuna wani mummunan yanayi da ke barazana ga rayuka, ilimi, hanyoyin samun abin rayuwa da kuma makomar miliyoyin ‘yan Najeriya. Ya ce hare-haren da ake kaiwa makarantu abin damuwa ne matuƙa domin makarantu wurare ne masu tsarki da ake rainon shugabannin gobe tare da ba su ilimin da zai ba su damar yi wa ƙasa hidima. A cewarsa, duk wani hari kan makaranta hari ne kai tsaye kan makomar Najeriya.
Dangane da haka, ya yi kira ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa, tare da ba da fifiko ga kare makarantu, al’ummomin karkara, manyan hanyoyi da sauran wuraren da ke cikin haɗari.
Ya tunatar da gwamnati cewa Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya tanadi cewa “tsaro da jin daɗin jama’a su ne babban manufar gwamnati.” Ya ce wajibi ne a fassara wannan tanadi zuwa aikace-aikacen da za su kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Domin magance kalubalen tsaro da ke ci gaba da sauyawa, Pantami ya ce akwai buƙatar gaggawa ta amfani da fasahohin zamani wajen tsaro. Ya ce hakan ya kamata ya haɗa da amfani da jirage marasa matuƙi (drones) domin sa ido kai tsaye a dazuka da wuraren da gwamnati ba ta da cikakken iko, amfani da taswirorin tauraron dan adam wajen gano maboyar ‘yan ta’adda da sansanonin masu aikata laifuka, tsarin gano fuska na zamani domin bibiyar hanyoyin sadarwar masu laifi, kayan aikin tattara bayanan geospatial, da kuma hanyoyin sadarwa na zamani da za su inganta saurin kai dauki.
Bugu da ƙari, ya jaddada cewa wajibi ne a sake fasalin tsarin tattara bayanan sirri da musayar su gaba ɗaya. Ya ce al’ummomin yankuna suna da muhimmiyar masaniya game da muhallansu, don haka ya kamata a haɗa su cikin tsari mai kyau na tattara bayanan sirri domin bai wa hukumomin tsaro damar hango barazana tun kafin ta afku, gano abubuwan da ke da alamar haɗari da kuma dakile hare-hare kafin su faru. A cewarsa, tattara bayanan sirri daga al’umma tare da goyon bayan fasaha da ƙwararrun ayyukan tsaro na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen yaƙi da ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka.
Pantami ya miƙa ta’aziyyarsa ga dukkan waɗanda hare-haren suka shafa da iyalansu, tare da kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da tabbatar da cewa an gano masu hannu a cikin waɗannan munanan laifuka, an kama su kuma an gurfanar da su a gaban shari’a.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya tona asirin masu aikata laifuka, masu ɗaukar nauyinsu, masu goyon bayansu da masu taimaka musu. Ya kuma roƙi Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya tare da kare ‘yan ƙasarta daga dukkan wani bala’i.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0