DA DUMI-DUMINSA: Kotu Ta Bada Umarnin Gwanjon Kadarorin Sirikin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Bisa Taurin Bashi

Jun 4, 2026 - 08:27
 0  0
DA DUMI-DUMINSA: Kotu Ta Bada Umarnin Gwanjon Kadarorin Sirikin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Bisa Taurin Bashi

Daga Saifullahi Lawal Imam

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bada umarnin yin gwanjon wasu kadarori mallakin tsohon ɗan majalisar tarayya, kuma Tsohon Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna, kuma Sirikin Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Muhammadu Buhari wato Alhaji Mahmood Sani Sha’aban (Danburam Zazzau), sakamakon wata takaddama ta bashi da ta daɗe tana gudana tsakaninsa da fitaccen ɗan kasuwar nan Alhaji Umar Faruk Abdullahi, a ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.

Kadarorin da kotun ta yi gwanjonsu sun haɗa da fili da gine-ginen da ke G.R.A Zaria, wadanda ke bayan gidansa da yake zaune, dake gaban Makarantar Sakandaren Therbow a Zariya, mai takardar Shaidar Mallaka (C of O) mai lamba KD 3984; da kuma fili da gine-ginen da ke kan Plot No. 3, Churchill Road, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 11226.

Sauran kadarorin sun haɗa da fili da gine-ginen da ke Tulips, mahadar MTD da ke gefen titin Queen Elizabeth, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 15052, da kuma kamfanin Mazari Nails Limited da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 6246.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala gwanjon, Mista Abdullahi Yahaya, SAN,wanda kuma shine lauyan mai kara Umar Faruk Abdullahi,ya ce abin da aka gudanar a ranar shi ne gwanjo da sayar da kadarorin wanda ake bin bashi kamar yadda hukuncin Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke Zariya ya tanada.

Ya ƙara da cewa kotun ta ƙwace kadarori guda biyar na wanda ake bin bashin, inda huɗu daga cikinsu suke a Zariya, yayin da ɗaya ke Kano.

Idan za a tuna ita wannan shari’ar ta samo asali ne daga wata yarjejeniyar bashi da aka kulla a shekarar 2018 tsakanin Hon. Sani Mahmud Sha’aban (Dan Buram Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi domin taimaka wa Sha’aban wajen warware wata matsala da ta shafi kama shi da tsare shi a gidan yari a kasar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a shekarar 2018.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, mai bin bashin ya bai wa Sha’aban rancen Dala miliyan ɗaya ta Amurka (US$1,000,000) da kuma Naira miliyan 11.2 ba tare da ruwa ko karin riba ba, bisa tsarin shari’ar Musulunci. Lauyoyin Sha’aban ne suka tsara kuma suka shaida yarjejeniyar, yayin da ɗansa ya sanya hannu a madadinsa, sa'ilin da shi kan shi Sani Sha'aban din bayan dawowar shi daga gidan yari ya sake sanya hannu don tabbatar da amincewarsa da yarjejeniyar.

Daga bisani, Sha’aban ya biya Dala 290,762 daga cikin bashin dala miliyan ɗaya, da ake bin shi amma daga baya ya ƙi biyan sauran kuɗin da suka rage. Daya daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar ita ce a biya bashin cikin watanni shida kuma da irin kuɗin da aka karɓa.

A ranar 12 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke GRA Zaria ta umarci Sani Sha’aban, tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna, da ya biya bashin Dala 709,238 da kuma Naira miliyan 11.2 ga Alhaji Umar Faruk Abdullahi.

Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace kadarorin Sha’aban da aka jingina a matsayin lamunin tabbatar da bashin.

Kwafin sahihin hukuncin da wakilinmu ya samu a cikin Shari’a mai lamba KDH/Z/12A/2024 ya nuna cewa kotun ta umarci Sha’aban, da ya biya dukkan kuɗaɗen da kotun ta yanke a cikin Naira da Dala ga Babban Magatakardar Babbar Kotun Jihar Kaduna.

Duk da Kokarin Daukaka Kara da Alhaji Sani Sha'aban yayi zuwa manyan Kotuna bai ci Nasara ba,inda ya rinka shan kaye a dukkan Shari'un Daukaka karar.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0