Goje Ya Shawarci A Bai Wa China Aikin Wutar Lantarki Na Shekara 20, Yayin Da Matsalar Wuta Ke Ci Gaba a Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma tsohon sanata, Danjuma Goje, ya sake jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan matsalar wutar lantarki a Najeriya, inda ya ce ƙasar za ta iya yin la’akari da ba wa ƙwararrun China damar gudanar da bangaren wutar lantarki na tsawon shekaru 20.
Ya bayyana wannan ra’ayi ne he said it during house seeting, inda ya ce matsalar wutar lantarki a Najeriya ta zama abin damuwa da ke shafar tattalin arziki, masana’antu, da rayuwar yau da kullum na ‘yan ƙasa.
Goje ya ce duk da ƙoƙarin da aka yi a baya wajen gyaran tsarin wutar lantarki, har yanzu ƙasar na fama da ƙarancin wuta mai dorewa. A cewarsa, ƙasar China na da ƙwarewa mai zurfi a harkar gine-ginen manyan ayyukan more rayuwa, tare da tsarin gudanarwa mai sauƙi da ƙarancin kuɗin aiki, wanda zai iya taimaka wa Najeriya wajen samun wutar lantarki mai inganci cikin ɗan lokaci.
Ya ƙara da cewa wannan ba yana nufin mika ikon ƙasar gaba ɗaya ba ne, sai dai tsarin haɗin gwiwa na wucin gadi da zai taimaka wajen gyara matsalar kafin daga bisani Najeriya ta dawo da cikakken iko.
Sai dai shawarar ta tayar da muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan Najeriya. Wasu na ganin hakan zai kawo sauƙi cikin gaggawa, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na iya rage ƙoƙarin gina ƙwararrun cikin gida da dogaro da kai.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0