Shugaban Kasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Sallami Shugaban NMDPRA, Ya Nada Sabo
Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sallamar nan take na Mista Saidu Mohammed daga mukaminsa na Babban Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Tsakani da Ƙasa (NMDPRA).
Haka kuma, shugaban ya nada Mista Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon Babban Shugaban hukumar. Sai dai wannan nadin na jiran amincewar Majalisar Dattawan Najeriya kafin ya fara aiki a hukumance.
Matakin na zuwa ne a wani yunƙuri na sake fasalin jagoranci a bangaren kula da harkokin mai domin inganta aiki da kuma tabbatar da daidaito a harkokin makamashi a ƙasar.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0