Tinubu Ya Kaddamar da Aikin Gyaran da Faɗaɗa Titin Gombe–Biu na Naira Tiriliyan 1.245
...Ministan Ayyuka Ya Yabi Gwamna Inuwa Yahaya Kan Ingantattun Ayyukan More Rayuwa
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da aikin sake gina tare da faɗaɗa titin Gombe–Biu mai tsawon kilomita 125, wanda kudinsa ya kai Naira tiriliyan 1.245, a wani babban mataki na bunƙasa ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Gabas.
An gudanar da bikin ƙaddamar da aikin ne a garin Liji da ke Jihar Gombe, inda Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, tare da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, suka wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen ƙaddamar da aikin.
Kamfanin Hi-Tech Construction Company ne zai aiwatar da aikin ta amfani da fasahar rigid pavement, kuma ana kallon aikin a matsayin wani gagarumin ci gaba bayan shekaru da dama da gwamnatocin baya suka kasa gyara wannan muhimmiyar hanyar.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa titin Gombe–Biu wata muhimmiyar hanyar tattalin arziki da zamantakewa ce da ke haɗa yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya da maƙwabtan ƙasashen Yammacin Afirka.
Ya ce aikin zai taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, sufuri, tsaro da kuma haɗin kan yankuna.
Gwamnan ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da aikin, yana mai bayyana hakan a matsayin wata alama ta ƙudurin gwamnatin tarayya na sabunta ababen more rayuwa da inganta ci gaban ƙasa.
“Ina tabbatar da cewa za mu yi aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ayyuka da kamfanin da ke gudanar da aikin domin tabbatar da an kammala shi cikin lokaci tare da bin ƙa’idojin inganci mafi girma domin amfanin al’umma na tsawon lokaci,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatar da ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya tuna cewa an fara gina titin ne tun shekarar 1962, sannan aka sake shimfiɗa shi a shekarar 1976, amma duk da muhimmancinsa ga yankin Arewa maso Gabas da Najeriya baki ɗaya, gwamnatocin baya sun kasa sake gina shi.
Ya kuma gode wa Ministan Ayyuka da mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa bisa goyon bayan da suka bayar, tare da yin kira da a ci gaba da samar da kuɗaɗen aikin da kuma sa ido domin tabbatar da nasarar aiwatar da shi.
Gwamnan ya bayyana cewa al’ummar Jihar Gombe na matuƙar godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa wajen bunƙasa jihar da yankin Arewa maso Gabas, yana mai cewa za su mayar da martani da cikakken goyon baya da kuri’u masu yawa a zaɓen shekarar 2027.
A nasa jawabin, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana aikin faɗaɗa titin a matsayin “kyautar Sallah” da Shugaba Tinubu ya bai wa al’ummar jihohin Gombe, Borno da ma yankin Arewa maso Gabas baki ɗaya.
Umahi ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan shugabanci nagari da kuma gagarumin ci gaban ababen more rayuwa da ya samar a Jihar Gombe, inda ya bayyana shi a matsayin “mai aiki cikin natsuwa kuma mutum mai kima.”
Ministan ya kuma bayyana cewa za a ƙara tsawon aikin daga kilomita 125 zuwa kilomita 139 bayan buƙatar da gwamnan ya gabatar na karkatar da hanyar ta bi ta Northern Bypass maimakon cikin gari, domin rage cunkoson ababen hawa da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci a muhimman wuraren tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na bai wa manyan ayyukan more rayuwa muhimmanci domin samar da damar tattalin arziki da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Shugabannin Kwamitocin Ayyuka na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da suka halarci taron sun yabawa Shugaba Tinubu bisa amincewa da aikin ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, tare da yabawa Gwamna Inuwa Yahaya da Ministan Ayyuka kan jajircewarsu wajen samar da ingantattun ayyukan more rayuwa.
Hakazalika, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Yamaltu/Deba, Hon. Inuwa Garba, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da aikin, tare da yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan ci gaba da fafutukar ganin an aiwatar da wannan muhimmin aiki.
A nasa bangaren, Sarkin Yamaltu, Alhaji Abubakar Aliyu, ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa magance matsalar da ta daɗe tana addabar yankin, yana mai tabbatar da samar da cikakken tsaro ga ma’aikatan aikin da kayan aikinsu.
Tun da farko, Manajan Daraktan Kamfanin Hi-Tech Construction Company, Mista Danny Abboud, ya tabbatar wa Gwamnatin Tarayya da al’ummar Arewa maso Gabas cewa za a aiwatar da aikin bisa ƙa’idojin da aka gindaya tare da kammala shi cikin lokacin da aka tsara.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0