JAMB Ta Fara Tantance Ƙananan ’Yan Takarar UTME da Suka Samu Sama da Maki 320
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa, Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB), ta fara tantance ’yan takarar da ba su kai shekarun shiga jami’a ba amma suka samu maki 320 ko sama da haka a jarabawar UTME ta shekarar 2026, ƙarƙashin tsarin da hukumar ta tanada na bai wa fitattun ɗalibai dama ta musamman.
Matakin ya biyo bayan damuwar da ta taso daga wasu ɗalibai da iyayensu, bayan da wasu daga cikin ƙananan ’yan takarar suka kasa ganin sakamakonsu a shafin JAMB, inda suka rika ganin saƙon “No Result Yet”.
A wata sanarwa da mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar, hukumar ta bayyana cewa riƙe sakamakon waɗannan ɗalibai ba matsalar fasaha ba ce, illa wani tsari ne da aka tanada domin tantance cancantarsu.
JAMB ta bayyana cewa tsarin shiga manyan makarantu a Najeriya ya tanadi cewa dole ne ɗalibi ya kai aƙalla shekara 16 kafin ranar 30 ga Satumba, 2026, kafin a ba shi gurbin karatu a jami’a ko wata makarantar gaba da sakandare.
Sai dai hukumar ta ce akwai wata ƙofa ta musamman ga ɗaliban da suka nuna bajinta ta fuskar karatu. A ƙarƙashin wannan tsari, duk ɗan takarar da bai kai shekarun shiga ba dole ne ya samu aƙalla maki 320 cikin 400 a UTME kafin a duba yiwuwar ba shi dama ta musamman.
JAMB ta ce duk wanda ya kai wannan matakin zai shiga wani ƙarin tantancewa, wanda zai haɗa da jarabawar post-UTME da sauran gwaje-gwajen tantance ilimi da ƙwarewa, domin tabbatar da cewa yana da cikakken shirin shiga jami’a.
Hukumar ta jaddada cewa manufar wannan tsari ita ce kiyaye ingancin ilimi tare da bai wa fitattun ɗalibai damar ci gaba da karatu tun da wuri.
Ta kuma buƙaci iyaye da masu kula da ɗalibai su kwantar da hankalinsu kan batun sakamakon da aka riƙe, tana mai tabbatar da cewa za a tuntubi duk wanda ya cika sharuddan wannan tsari domin ci gaba da tantancewa.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a faɗin ƙasa kan shekarun da suka dace ɗalibai su shiga jami’a, inda JAMB ke nanata cewa shekara 16 ita ce ƙa’ida, yayin da damar ta musamman za ta kasance ne kawai ga ƙalilan daga cikin fitattun ɗalibai.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0