An Ƙirƙiri Sa Hannuna na Bogi — Nafiu Bala Ya Musanta Takardar Murabus daga ADC
Shugaban ɓangaren jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafiu Bala, ya fito fili ya ƙaryata rahotannin da ke yawo cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Bala ya bayyana cewa takardar murabus ɗin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da wasu hanyoyi ba tasa ba ce ko kaɗan. Ya ce an ƙirƙiri sa hannunsa ne na bogi domin haddasa rikici da ruɗani a cikin jam’iyyar.
“Ban rubuta wata takardar murabus ba, kuma ban ajiye aikina ba. Har yanzu ina kan kujerata kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.
Wannan martani na Bala na zuwa ne bayan hukuncin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta yanke a ranar Laraba, dangane da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar ADC.
A halin yanzu, rikicin cikin gida a jam’iyyar ADC na ci gaba da ɗaukar sabon salo, inda ɓangarori daban-daban ke bayyana ra’ayoyinsu kan wanda ya kamata ya jagoranci jam’iyyar. Lamarin na ci gaba da haifar da cece-kuce tsakanin magoya baya da ‘yan siyasa, tare da jawo hankalin jama’a a fagen siyasar ƙasa.
Masu sa ido kan al’amuran siyasa na ganin cewa yadda rikicin ke ƙara tsananta na iya yin tasiri ga makomar jam’iyyar, musamman a daidai lokacin da ake shirin tunkarar manyan zaɓuɓɓuka a ƙasar.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0