‎Da Dumi Dumi: Ana zargin Farfesa Isa Ali Pantami da sayen tsohon Hadimin Inuwa Yahaya.

Oct 8, 2026 - 20:56
Oct 8, 2026 - 20:56
 0  1
‎Da Dumi Dumi: Ana zargin Farfesa Isa Ali Pantami da sayen tsohon Hadimin Inuwa Yahaya.

Wata majiya da kafar yaɗa labarai ta Global Focus Hausa ta bayyana cewa ta samu wasu bayanai da ke zargin cewa Ahmed Shuaibu Gara, wanda ake alakanta shi da tsohon mai taimakawa Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya karɓi kuɗi har Naira miliyan 50 domin ci gaba da kai hare-haren kalamai da cin mutuncin wasu manyan mutane a jihar Gombe.

‎A cewar majiyar Global Focus, Ahmed Shuaibu Gara ya shahara wajen wallafa ko yaɗa kalamai masu zafi kan wasu daga cikin manyan mutane a Jihar Gombe, ciki har da sarakuna, malaman addini, manyan ma’aikatan gwamnati, ’yan kasuwa da sauran al’umma da suka samu ci gaba.

‎Majiyar ta kuma yi zargin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ne ya ba Ahmed Shuaibu Gara kuɗin da yawansu ya kai Naira miliyan 50, domin ya ci gaba da wannan dabi’a.

‎Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu martanin Ahmed Shuaibu Gara ko Farfesa Isa Ali Pantami kan wannan zargi ba.

‎Ana kuma buƙatar dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su samu damar bayyana matsayinsu domin jama’a su samu cikakken bayani kan batun.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0
Abubakar Yahaya A Journalist and Human Rights Activist.