Kungiyar Arewa Progressive Media Ta Karrama Tsohon Daraktan Hukumar Ƙididdiga a Jihar Gombe

Jul 26, 2026 - 19:02
Jul 26, 2026 - 19:08
 0  6
Kungiyar Arewa Progressive Media Ta Karrama Tsohon Daraktan Hukumar Ƙididdiga  a Jihar Gombe

Kungiyar Arewa Progressive Media ta karrama fitaccen ɗan asalin Jihar Borno, Alhaji Dr. Mohammed Musa Tumala, tsohon Daraktan Hukumar Ƙididdiga, a wani gagarumin biki da aka gudanar a Jihar Gombe.

An gudanar da wannan karramawa ne a yayin wata ziyarar kashin kai da Dr. Tumala ya kai jihar, inda shugabanni da mambobi tare da magoya bayan kungiyar suka halarci taron domin nuna girmamawa da goyon bayansu.

Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Kungiyar, Komarade Haruna Abdullahi, ya bayyana cewa manufar wannan taro ita ce girmama mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa al'umma hidima. Ya ce kungiyar ta dauki lokaci mai tsawo tana nazari da tantance mutanen da suka cancanci wannan karramawa, domin hakan na kara musu kwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ci gaban kasa.

Har ila yau, ya bayyana irin gudummawar da Dr. Mohammed Musa Tumala ya bayar ga al'umma, musamman a bangaren tallafa wa marasa galihu, marayu, mata da matasa, tare da samar da hanyoyin da za su dogara da kansu domin inganta rayuwarsu.

A nasa jawabin, Shugaban Arewa Progressive Media, Comrade Sani Bello Yusuf, ya bayyana Dr. Tumala a matsayin uba, jagora kuma abin koyi ga matasa, 'yan siyasa da masu sana'o'i. Ya ce Dr. Tumala mutum ne mai kishin kasa wanda ya sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa wajen taimaka wa al'umma, musamman mata da matasa, domin samun ingantacciyar rayuwa.

A nasa bangaren, Alhaji Dr. Mohammed Musa Tumala ya fara da godiya ga Allah Madaukakin Sarki, sannan ya mika godiyarsa ga kungiyar Arewa Progressive Media bisa wannan gagarumar karramawa. Ya yi addu'ar Allah Ya sanya albarka a ayyukan shugabannin kungiyar tare da ba su ikon ci gaba da riko da gaskiya, adalci da amana.

Daga karshe, Dr. Tumala ya yi kira ga 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauran masu hannu da shuni da su kara zage damtse wajen shiga ayyukan ci gaban al'umma ba tare da nuna son kai ba, domin hada kai wajen gina kasa mai dorewa da walwalar jama'a.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0