Shugaban Kasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Amince da Biyan Naira Tiriliyan 3.3 Don Gyaran Wutar Lantarki a Najeriya
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani shirin biyan bashin da ya kai naira tiriliyan 3.3 domin magance matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki a ƙasar.
Wannan mataki na cikin shirin gyaran harkar lantarki na gwamnati wanda aka sani da Presidential Power Sector Financial Reforms Programme. An dauki wannan mataki ne bayan kammala nazari kan tarin basussukan da suka yi shekaru sama da goma suna jawo cikas ga samar da wutar lantarki mai dorewa.
Bincike ya nuna cewa basussukan sun taru ne tsakanin watan Fabrairun 2015 zuwa Maris 2025. Bayan tantancewa, an amince da naira tiriliyan 3.3 a matsayin cikakken biyan bashin domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin.
Tuni aka fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar jimillar naira tiriliyan 2.3. Gwamnatin tarayya ta riga ta tanadi naira biliyan 501 domin fara biyan kudaden, inda aka riga aka fitar da naira biliyan 223, yayin da ake ci gaba da sauran biya.
Ana sa ran wannan shiri zai inganta samar da wutar lantarki a ƙasar, domin zai taimaka wajen tabbatar da dorewar aiki ga kamfanonin samar da wuta. Hakan zai kara kwarin gwiwa ga masu zuba jari, samar da ayyukan yi, da kuma inganta ayyukan sabis ga al’umma.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, ta bayyana cewa shirin ba wai kawai biyan tsofaffin basussuka ba ne, har ma yana da nufin dawo da amincewa a bangaren wutar lantarki.
Ta ce gwamnati na kuma aiwatar da wasu gyare-gyare kamar inganta tsarin mita da kuma tsarin kudin wuta da ya danganci ingancin sabis da ake samu.
Haka kuma, gwamnati na bai wa kamfanoni, masana’antu da kananan sana’o’i fifiko wajen samar da wutar lantarki, domin hakan na da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
A karshe, Shugaba Tinubu ya yaba wa duk masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen cimma wannan nasara, tare da sanar da cewa mataki na gaba na shirin (Series II) zai fara a cikin wannan zangon shekara.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0