Jagoran Juyin-Juya-Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, Ya yi Jawabi na Farko a Yau Alhamis
Cikin jawabinsa ya bayyana:
“A farkon jawabina, ina miƙa ta’aziyya ga jagorana, Imam Mahdi, a kan shahadar rai mai raɗaɗi ta Babban Jagoran juyin-juya-hali, mai daraja da hikima, Khamenei.
Ni, bawanku, Seyyed Mojtaba Hosseini Khamenei, na samu labarin sakamakon zaɓen Majalisar Masana a lokaci guda da ku ta hanyar kafofin yaɗa labarai na Jamhuriyar Musulunci.
A gare ni, ɗaukar matsayin da manyan jagorori biyu, Ayatollah Ruhollah Khomeini da Khamenei suka zauna a kai, aiki ne mai matuƙar wahalar gaske.
Bayan fiye da shekaru 60 na gwagwarmaya a tafarkin Allah, tare da sadauƙar da dukannin jindaɗi da walwala, ya kasance madubi mai haske, kuma mutum mai daraja, ba kawai a wannan zamani ba, har ma a tarihin jagororin wannan ƙasa.
Na samu darajar ziyartar gangar jikinsa bayan shahadarsa; abin da na gani shi ne mutum wanda ya tsaya ƙyam (a kan tafarki), kuma an gaya min cewa hannunsa ɗaya daga cikin hannunsa mai lafiya, ya kasance a damtse."
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0