๐Ÿ”ฅ Gobara Ta Tashi a Sashen Ofishin Shugaban Maโ€™aikatan Gwamnatin Tarayya a Abuja

๐Ÿ”ฅ Gobara Ta Tashi a Sashen Ofishin Shugaban Maโ€™aikatan Gwamnatin Tarayya a Abuja

Mar 9, 2026 - 11:13
Mar 9, 2026 - 11:14
 0  14
๐Ÿ”ฅ Gobara Ta Tashi a Sashen Ofishin Shugaban Maโ€™aikatan Gwamnatin Tarayya a Abuja

An shiga cikin tashin hankali a harabar Federal Secretariat Complex a safiyar Litinin bayan da gobara ta tashi a wani sashe na ofishin Office of the Head of the Civil Service of the Federation.

Rahotanni daga shaidun gani da ido sun bayyana cewa an fara lura da gobarar da misalin karfe 8:20 na safe, lamarin da ya janyo fargaba ga maโ€™aikata da sauran mutanen da ke cikin harabar.

Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda hayaki mai kauri baki ke tashi daga sashen da gobarar ta shafa.

An ce lamarin ya faru ne a Section C na ginin da ke cikin harabar Federal Secretariat Complex a Abuja.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, yayin da jamiโ€™an kashe gobara ke ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0