Zargin DG Na Bogi: Adeyemi Ya Ce Nadin Sa Ingantacce Ne, Ya Ce Kotu Za Ta Wanke Shi
Mutumin da ke ikirarin cewa shi ne Darakta Janar na abin da ake kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) da kuma Presidential Economic Advisory Council, Adeniyi Adeyemi Matthew, ya dage cewa nadin da aka ba shi na gaskiya ne, duk da cewa Fadar Shugaban Kasa ta bayyana shi a matsayin mai damfara.
Adeyemi, wanda ake tuhuma da laifukan haɗa baki, ƙirƙirar takardun bogi da kuma yin sojan gona, ya ce shari'ar tana gaban kotu kuma yana da cikakken yaƙinin cewa za a wanke shi daga zarge-zargen da ake masa.
Ya bayyana hakan ne a wata hira ta wayar tarho da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television a ranar Alhamis.
Da aka tambaye shi ko yana guje wa hukuma, Adeyemi ya ce ba haka ba ne. Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya fuskanci shari'a, yana mai cewa idan yana da laifi kotu ta hukunta shi, idan kuma ba shi da laifi kotu za ta tabbatar da hakan.
Adeyemi ya ce yana da takardar nadin aiki, amma saboda shari'ar tana gaban kotu ba zai iya bayyana cikakkun bayanai ba. Ya kuma ce yana fama da rashin lafiya kuma yana karɓar magani.
Game da zargin cewa shi mai laifi ne, Adeyemi ya musanta hakan, yana mai cewa kotu ce kawai za ta yanke hukunci kan lamarin.
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su yi tunani kan zargin cewa hukumar ba ta wanzu. A cewarsa, da ace hukumar ba ta da tushe, ba zai iya zagayawa yana ganawa da shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati na kusan shekara uku ba tare da an dakatar da shi ba.
Rahotanni sun nuna cewa Adeyemi ya shafe watanni yana gudanar da ayyuka a ƙarƙashin sunan PFIPC, inda aka ce ofishin ya shirya manyan taruka tare da hulɗa da hukumomin gwamnati. Haka kuma, an ce hukumar ta samu kasafin kuɗi na naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026.
Sai dai a ranar Laraba, Fadar Shugaban Kasa ta musanta ikirarin Adeyemi, tare da bayyana shi a matsayin mai yin sojan gona da ake tuhuma da ƙirƙirar takardun bogi da kuma kwaikwayon jami'an gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, Fadar Shugaban Kasa ta ce binciken 'yan sanda ya gano cewa Adeyemi ya ƙirƙiri takardar nadin aiki ta bogi. Haka kuma, an zarge shi da gudanar da wata hukuma da ba ta wanzu tare da buɗe asusun banki 34, ciki har da tara da aka ce an buɗe su da sunayen hukumomin gwamnati da ba su da wanzuwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kama Adeyei ne a ranar 27 ga Oktoba, 2025, bayan ƙorafin da Gbajabiamila ya shigar ga hukumomin tsaro. Daga bisani, rundunar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da shi tare da wasu mutum biyu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da haɗa baki, ƙirƙirar takardun bogi da yin sojan gona.
An kuma bayyana cewa za a ci gaba da sauraron shari'ar a ranar 27 ga Yuli, 2026.
A wani ɓangaren kuma, Adeyemi ya zargi Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa da neman naira biliyan 27.4, wanda ya ce ya kai kashi 48 cikin 100 na kuɗin da aka tanada domin fara aikin hukumar. Haka kuma ya yi zargin cewa an karɓi naira miliyan 400 ta hannun wani domin sauƙaƙa masa samun nadin, inda ya ce har yanzu akwai saura naira miliyan 200.
Adeyemi ya buƙaci Shugaban Ƙasa da ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken waɗannan zarge-zarge, tare da duba takardun hukumomin da ake takaddama a kansu da kuma bayyana sakamakon binciken ga jama'a. Ya kuma buƙaci Femi ya ajiye mukaminsa har sai an kammala binciken.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0