Tarihin Yadda Mafarkin Ɗan Kwallon Kasar Italiya Alessandro Nesta Ya Fara – Labarin
Tarihin Yadda Mafarkin Ɗan Kwallon Kasar Italiya Alessandro Nesta Ya Fara – Labarin
Tsohon fitaccen ɗan wasan baya na ƙasar Italiya, Nesta, ya bayyana yadda rayuwarsa da burinsa na zama ɗan ƙwallon ƙafa suka fara tun yana ƙarami a wani ƙaramin ƙauye.
A cewarsa, mahaifinsa ya kasance ma’aikaci a kamfanin jirgin ƙasa, yayin da mahaifiyarsa, Maria Laura, ta kasance uwar gida. Sun taso ne a matsayin iyali mai sauƙin rayuwa daga ƙauyen Collevecchio da ke lardin Rieti a ƙasar .
Nesta ya ce komai ya fara ne a shekarar 1984 lokacin da mahaifinsa ya kai babban ɗan’uwansa Fernando makarantar koyon ƙwallon ƙafa domin yi masa rajista. Sai dai shi kuma ya fashe da kuka saboda yana jin an bar shi a baya. Daga ƙarshe mahaifinsa ya biya ƙarin kuɗi domin shi ma ya samu damar yin rajista duk da cewa yana da shekara takwas kacal.
Bayan wasu watanni, wani mai gano hazaka na ƙungiyar mai suna Francesco Rocca ya tuntubi iyalinsu. Amma iyalinsu ba su ɗauki maganar da muhimmanci ba saboda dukansu magoya bayan ne.
Abin mamaki ya faru ne bayan wasu kwanaki lokacin da shugaban ƙungiyar Roma a wancan lokaci, , ya je gidansu da kansa. Ya ajiye kuɗi miliyan goma na lire a kan tebur — adadi mai yawa a lokacin — yana cewa suna son Nesta ya koma Roma.
Sai dai mahaifinsa ya ƙi amincewa da tayin cikin tsauri, yana cewa:
“Ɗana ya sanya rigar Roma? Ba zai yiwu ba. Gara ma na mutu kafin hakan ta faru.”
Nesta ya ce shi ma ya goyi bayan shawarar mahaifinsa, yana nuna biyayya da kauna ga ƙungiyar Lazio. Lokacin da mahaifinsa ya tambaye shi ko yana son Lazio, sai ya amsa ba tare da jinkiri ba cewa: “Eh, wannan shi ne mafarkina.”
Daga nan ya shiga sansanin horaswa na San Basilio tare da yara sama da 300 yana ɗan shekara tara. A farko yana buga wasa a tsakiyar fili, har ma ya taba gwada wasa a matsayin winger na dama.
Sai dai wani gagarumin girma da jikinsa ya yi — santimita 22 cikin shekara guda — ya sa yana fama da ciwon gwiwa da ƙugu. Wannan ne ya sa aka gwada shi a matsayin mai tsaron baya na tsakiya, wato center-back, inda daga nan ya gano ainihin matsayinsa a filin wasa.
A lokacin bazara kuma ya samu horo a ƙarƙashin mai horo mai tsauri, , wanda ake kira Mimmo Caso. Nesta ya ce daga wurinsa ya koyi yadda ake karanta sararin fili da kuma yadda ake taka rawar tsaron zone.
Ya ce ɗaya daga cikin mafi girman lokutan rayuwarsa shi ne ranar da ya fara sanya kambin kyaftin na . Duk da haka, mafarkinsa na ci gaba da zama a Lazio har abada bai cika ba, domin ƙungiyar ta shiga matsalar kuɗi wanda ya sa dole ya bar ta.
“Ba haka nake so labarin ya ƙare ba,” in ji Nesta, “amma soyayyata ga Lazio ba ta taɓa ƙarewa ba. Duk lokacin da na kalli sararin sama na ga launin sa, sai na tuna da launin Lazio — kuma za su kasance a cikin zuciyata har abada.”
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0