Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko na Jihar Gombe Ta Ƙarfafa Haɗin Guiwa da Masarautar Kaltungo

Jun 14, 2026 - 13:24
 0  5
Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko na Jihar Gombe Ta Ƙarfafa Haɗin Guiwa da Masarautar Kaltungo

Gombe, Nigeria 🇳🇬  Yuli 14, 2026

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Gombe (Primary Health Care Board), Dr. Ahmad Ya'u Kashere, ya kai ziyarar aiki zuwa Masarautar Kaltungo da ke Ƙaramar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe a ranar Alhamis.

Dr. Ahmad Ya'u Kashere ya samu rakiyar wasu daga cikin manyan ma'aikatan hukumar yayin ziyarar, inda tawagar ta sauka a fadar Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad Umar, domin neman ƙarin haɗin kai da goyon baya wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya a matakin farko.

Da yake jawabi a fadar Mai Kaltungo, Dr. Ahmad Ya'u Kashere ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa irin jajircewa da ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen bunƙasa harkokin kiwon lafiya da tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta ba fannin lafiya muhimmanci na musamman, musamman ta fuskar inganta ayyukan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, domin tabbatar da cewa al'umma sun samu ingantaccen kulawar lafiya a yankunansu.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa haɗin kan sarakunan gargajiya na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin gwamnati na inganta kiwon lafiyar jama'a, musamman ta fuskar wayar da kan al'umma da ƙarfafa su wajen amfani da cibiyoyin kiwon lafiya.

A nasa jawabin, Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad Umar, ya gode wa tawagar bisa wannan ziyara, yana mai bayyana cewa masarautar za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga shirye-shiryen kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar al'umma.

Ya kuma tabbatar da cewa al'ummar masarautar Kaltungo a shirye suke su ci gaba da mara wa gwamnati da hukumomin lafiya baya, musamman wajen bunƙasa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko.

Bayan kammala ziyarar fadar Mai Kaltungo, Dr. Ahmad Ya'u Kashere da tawagarsa sun kai ziyarar duba aiki zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Matakin Farko da ke Kalari da Wange duk a Ƙaramar Hukumar Kaltungo.

A yayin ziyarar, shugaban hukumar ya nuna gamsuwa da yadda ma'aikatan cibiyoyin guda biyu ke gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da jajircewa. Ya yabawa ma'aikatan tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da aiki cikin gaskiya, riƙon amana da kyakkyawar mu'amala da marasa lafiya domin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga al'umma.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya da samar da yanayin aiki mai kyau ga ma'aikata domin tabbatar da kyakkyawan sakamako a fannin lafiya.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0