Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kuɗin 2026 na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Wa’adin Kasafin 2025

Apr 17, 2026 - 14:49
 0  8
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kuɗin 2026 na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Wa’adin Kasafin 2025

Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, inda aka amince da jimillar kuɗi har Naira tiriliyan 68.32, tare da tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin 2025 zuwa ranar 30 ga Yuni, 2026.

Sabon kasafin ya ƙunshi manyan rabe-raben kuɗi da suka haɗa da Naira tiriliyan 4.799 don kudaden doka (statutory transfers) da kuma Naira tiriliyan 15.8 domin biyan basussuka. Haka kuma, an ware Naira tiriliyan 15.4 don kuɗaɗen gudanarwa (recurrent expenditure), yayin da aka tanadi Naira tiriliyan 32.2 don ayyukan ci gaba a ƙarƙashin Asusun Ci Gaba (Development Fund).

Kasafin ya nuna cewa kusan kashi 50 cikin 100 na kuɗin an ware shi ne don ayyukan gine-gine da ci gaba, wanda ke nuna aniyar gwamnati na inganta ababen more rayuwa, tabbatar da daidaiton tattalin arziki, tsaro, da kuma ci gaban da ya shafi kowa da kowa.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, kasafin ya daidaita tsakanin biyan wajibai na doka, biyan basussuka, da kuma saka jari a muhimman ayyukan da za su ƙara haɓaka tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya amince da dokar gyaran kasafin (Appropriation Amendment Bill), wadda ta tsawaita wa’adin ɓangaren ayyukan ci gaba na kasafin 2025 daga ranar 31 ga Maris zuwa 30 ga Yuni, 2026. Wannan mataki na nufin tabbatar da kammala muhimman ayyuka da ke gudana a sassa daban-daban na ƙasar.

Ana sa ran tsawaita wa’adin zai ba Ma’aikatu, Hukumomi da Sassa (MDAs) damar kammala ayyukan da suka kusa ƙarewa, ƙara yawan ayyukan da ake kammalawa, da kuma amfani da kuɗin jama’a yadda ya dace.

Da zarar kasafin 2026 ya fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, Gwamnatin Tarayya za ta fara cikakken aiwatar da shi bisa tsarin manufofin “Renewed Hope Agenda.”

Shugaba Tinubu ya umarci dukkan MDAs da su tabbatar da gaskiya, bin ƙa’ida, da kuma amfani da kuɗi yadda ya kamata, tare da mayar da hankali kan samun ƙimar kuɗi (value for money) da kuma kammala ayyuka a kan lokaci.

Haka kuma, ya yaba wa Majalisar Ƙasa bisa gaggauta nazari da amincewa da kasafin, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa wajen bunƙasa ƙasa.

Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa gyaran harkokin kuɗi, inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, samar da ayyukan yi, da kuma faɗaɗa shirye-shiryen tallafin jin daɗin al’umma.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0