Tsohon Gwamnan Jahar Kano Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi Nafiu Bala: “Matakansa na iya illata dimokuraɗiyyar Najeriya

Apr 7, 2026 - 19:01
Apr 7, 2026 - 19:40
 0  5
Tsohon Gwamnan Jahar Kano Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi Nafiu Bala: “Matakansa na iya illata dimokuraɗiyyar Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kakkausar suka ga Nafiu Bala, yana mai cewa gazawarsa wajen amsa gayyata da kuma wasu matakai da yake ɗauka na iya jefa dimokuraɗiyyar Najeriya cikin hadari.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa, wadda ta karade kafafen sadarwa a ranar Talata.

A cewarsa, ya gayyaci Bala domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), amma Bala bai girmama gayyatar ba. Kwankwaso ya bayyana hakan a matsayin rashin mutunci da kuma rashin kishin cigaban siyasa.

“Na yi ƙoƙarin ganin mun zauna domin mu tattauna yadda za a gina jam’iyya mai ƙarfi da kuma kare dimokuraɗiyya, amma abin takaici ya ƙi amsa gayyata,” in ji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa irin waɗannan halaye na rashin haɗin kai da biyayya ga tsarin jam’iyya na iya haifar da rikice-rikice a siyasar ƙasa, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai domin inganta dimokuraɗiyya.

Kwankwaso, wanda ya fice daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa ADC a ranar 30 ga Maris, 2026, ya ce yana da burin ganin an gina jam’iyya mai ƙarfi wadda za ta zama madadin nagari ga ‘yan Najeriya.

Ya kuma yi kira ga shugabanni da ‘yan siyasa da su guji matakan da ka iya haifar da rabuwar kai, yana mai cewa hadin kai da mutunta juna su ne ginshiƙan cigaban dimokuraɗiyya a ƙasa.

A ƙarshe, Kwankwaso ya jaddada cewa zai ci gaba da aiki tare da duk masu kishin ƙasa domin tabbatar da cewa dimokuraɗiyyar Najeriya ta samu karɓuwa da inganci a idanun duniya.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0