INEC Ta Sauya Jadawalin Zaben 2027, Ta Tsawaita Wa’adin Mika Rajistar Mambobin Jam’iyyu
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato Independent National Electoral Commission (INEC), ta sanar da sake duba jadawalin shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, inda ta tsawaita wa’adin mika rajistar mambobin jam’iyyun siyasa.
A wata ganawa da hukumar ta yi da jam’iyyun siyasa a ranar Talata, 24 ga Maris, 2026, an nuna damuwa kan gajeren lokacin da aka ware domin mika rajistar mambobin jam’iyyun, wanda a baya aka tsara daga 1 ga Afrilu zuwa 21 ga Afrilu, 2026.
Sakamakon haka, INEC ta amince da daidaita lokacin domin ya dace da sharuddan da Sashe na 77(4) na dokar zaɓe ta 2026 ya tanada, tare da bai wa jam’iyyun damar tsara lokutan gudanar da zaɓen fidda gwani (primaries) dinsu da kansu.
Hukumar ta bayyana cewa jam’iyyun siyasa za su iya gudanar da zaɓen fidda gwani daga ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, tare da jaddada muhimmancin bin wannan jadawali domin tabbatar da sahihin tsarin zaɓe.
Haka kuma, an umurci jam’iyyun da su tabbatar sun mika rajistar mambobinsu ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fidda gwani nasu. Wannan ya sa aka tsawaita wa’adin ƙarshe na mika rajistar zuwa ranar 10 ga Mayu, 2026, maimakon 21 ga Afrilu da aka tsara a baya.
Sanarwar ta fito ne daga Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, a ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0