ƊAN MAJALISAN DATTAWAWA NA GOMBE TA KUDU YA FICE DAGA JAM'IYAR APC BAYAN KIN AMINCEWA DA TSARIN “CONSENSUS”

May 9, 2026 - 15:55
 0  1
ƊAN MAJALISAN DATTAWAWA NA GOMBE TA KUDU YA FICE DAGA JAM'IYAR APC BAYAN KIN AMINCEWA DA TSARIN “CONSENSUS”

Wani sabon rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC a jihar Gombe bayan Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Siyako Anthony Yaro, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa matakin nasa ya biyo bayan rashin amincewarsa da tsarin zaɓen “consensus” da shugabannin APC a jihar suka amince da shi domin shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027. 

An ce rikicin ya fara ne bayan shugabannin APC a jihar karkashin jagorancin gwamna suka fara tantance wasu ‘yan takara da suka fi so ba tare da gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye ba. Wannan mataki ya haddasa rashin jituwa tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar, inda wasu suka bayyana tsarin a matsayin rashin adalci da tauye dimokuraɗiyya a cikin APC. 

Sanata Siyako Anthony Yaro, wanda ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda aka gudanar da lamarin, ya ce ba zai amince da duk wani tsari da zai hana ‘yan jam’iyya damar fafatawa cikin gaskiya da adalci ba.

Majiyoyi daga kusa da sanatan sun tabbatar da cewa ya riga ya koma jam’iyyar PDP domin ci gaba da fafutukar siyasarsa. Wannan sauyin sheƙa na zuwa ne a daidai lokacin da APC ke fama da rikice-rikicen cikin gida a Gombe, yayin da wasu fitattun ‘yan siyasa irin su Muhammad Danjuma Goje da magoya bayan Isa Pantami suma suka nuna rashin amincewa da tsarin “consensus” ɗin. 

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan rikici na iya raunana APC a Gombe kafin babban zaɓen 2027, musamman idan manyan jiga-jigan jam’iyyar suka ci gaba da ficewa ko nuna rashin biyayya ga shugabancin jam’iyyar.

Har yanzu shugabannin APC a jihar ba su fitar da cikakken martani kan ficewar Sanata Siyako Anthony Yaro daga jam’iyyar ba.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0