Adamu Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Ya Koma Jam’iyyar ADC

Mar 12, 2026 - 12:46
 0  7
Adamu Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Ya Koma Jam’iyyar ADC

Wani matashi dan siyasa a Najeriya, Adamu Atiku Abubakar, ya fice daga Peoples Democratic Party (PDP) a hukumance tare da ayyana komawarsa zuwa African Democratic Congress (ADC).

Adamu Atiku Abubakar ya sanar da wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa ya dauki wannan shawara ne bayan nazari mai zurfi kan halin da siyasa da kuma tsarin jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu.

Ya ce komawarsa jam’iyyar ADC wani mataki ne na ci gaba da fafutukar kawo sauyi mai anfani ga al’umma da kuma kara bada gudunmawa wajen gina kasa ta hanyar siyasa mai tsafta da gaskiya.

A cewarsa, jam’iyyar ADC tana ba da damar sabbin tunani da sabbin dabaru wajen tafiyar da siyasa, wanda hakan zai ba shi damar ci gaba da aiki tare da masu kishin kasa domin bunkasa dimokuradiyya da ci gaban Najeriya.

Adamu Atiku Abubakar ya kuma gode wa shugabanni da magoya bayan sa da suka tsaya tare da shi tun lokacin da yake PDP, yana mai cewa zai ci gaba da aiki tare da su domin cimma burin da suka sanya a gaba.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan sauya sheka na iya kara zafafa harkokin siyasa yayin da ake tunkarar zabukan shekarar 2027, inda jam’iyyu ke ci gaba da kokarin karfafa karfinsu da jawo sababbin mambobi.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0