Motar Dakon Yashi Ta Kwace Ta Fasa Kofar Gidan Gwamnatin Gombe Mai Darajar Miliyoyin Naira
Wata babbar mota dauke da yashi ta kwace tare da yin karo da sabuwar kofar shiga Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, lamarin da ya janyo babbar barna ga kofar da aka gina kwanan nan da kudade masu yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa motar ta rasa yadda za a shawo kanta ne kafin ta afka cikin kofar, inda ta lalata wani bangare mai muhimmanci na ginin. Duk da girman hadarin, direban motar ya samu raunuka kadan ne kawai.
Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa motar ta kwace ba, amma ana kyautata zaton matsalar birki ko sakacin direba na iya kasancewa cikin abubuwan da suka haddasa hadarin.
Jami’an tsaro da masu bada agajin gaggawa sun isa wurin domin duba halin da ake ciki tare da fara bincike kan musabbabin aukuwar lamarin.
Hukumomin jihar sun ce za su dauki matakan da suka dace domin gyara barnar da aka yi da kuma hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0