Hon. Zakariyya Jidda Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 20,740,000 Ga Jam’iyyar APC Da ‘Yan Jam’iyya A Jahar Gombe

Mar 9, 2026 - 20:37
Mar 10, 2026 - 13:22
 0  7
Hon. Zakariyya Jidda Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 20,740,000 Ga Jam’iyyar APC Da ‘Yan Jam’iyya A Jahar Gombe

A wata muhimmiyar ziyara da ya kai ofishin jam’iyyar APC a jahar Gombe, Hon. Zakariyya Jidda ya gana da shugabannin jam’iyya tare da mata da matasa ‘yan jam’iyyar, inda aka tarbe shi cikin farin ciki da girmamawa. A yayin ziyarar, ya nuna karamci ta hanyar bayar da tallafin kudi domin karfafa ayyukan jam’iyyar da kuma tallafawa shugabannin jam’iyya a matakin tushe.

A cikin rabon kudaden, shugabannin jam’iyyar APC a kananan hukumomin Kwami da Funakaye, wadanda ke da Ward guda 10 kowacce tare da shugabanni 27 a kowanne Ward, sun samu Naira dubu 20,000 kowanne. Hakan yazama jimillar Naira 5,400,000 a kowacce karamar hukuma.

Haka kuma, a Gombe Local Government wacce ke da Ward guda 11, shugabannin jam’iyya guda 27 a kowanne Ward sun samu Naira dubu 20,000 kowanne, wanda ya kai jimillar Naira 5,940,000.

Baya ga wannan tallafi, Hon. Zakariyya Jidda ya kuma bai wa APC Social Media Team kyautar Naira Miliyan 1,000,000 domin karfafa musu gwiwa wajen yada ayyukan maigirma Gwamna da manufofin jam’iyya. Haka kuma ya tallafawa matasa da mata da suka halarci taron da Naira dubu 500,000 kowanne, wanda suma jimillar yazama Naira Miliyan 1,000,000 hakan ya kara sanya farin ciki da annashuwa a wajen taron.

Haka zalika, daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi akwai wasu daga cikin State Excos na jam’iyyar APC da suka halarci wannan zama, mutum goma a jimilla, inda kowannensu ya samu kyautar Naira dubu 200,000, wanda jimillar kudin ya kai Naira Miliyan 2,000,000.

A yayin jawabinsa, Hon. Zakariyya Jidda ya yabawa maigirma Gwamnan Jahar Gombe, Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa irin jajircewarsa da kokarinsa wajen kawo ci gaba a fannonin rayuwa daban-daban a jahar. Ya bayyana cewa ayyukan cigaba da tsare-tsaren da gwamnan ke aiwatarwa sun kara bunkasa jahar Gombe tare da inganta rayuwar al’umma, inda ya kuma jaddada cikakken goyon bayansa ga jagorancin gwamnan

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0