Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Ba da Hakuri Kan Jinkirin Sakin Sakamakon jarrabawar UTME, Tayiko Gargadi Kan Magudin Sakamako

Apr 19, 2026 - 11:51
 0  12
Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Ba da Hakuri Kan Jinkirin Sakin Sakamakon jarrabawar UTME, Tayiko Gargadi Kan Magudin Sakamako

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta ba da hakuri ga ɗalibai da iyaye kan jinkirin da aka samu wajen sakin sakamakon jarabawar UTME na bana.

Hukumar ta bayyana cewa jinkirin ya faru ne sakamakon ƙarin bincike da take yi domin tabbatar da ingancin sakamakon da kuma hana duk wani nau’i na magudi.

JAMB ta kuma yi gargadi ga ɗalibai da jama’a gaba ɗaya da su guji duk wata hanya ta sauya ko ƙirƙirar sakamakon jarabawa, tana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa doka.

Hukumar ta jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan harkokin jarabawa a ƙasar.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0