Tinubu Ya Kafa Asusun na Musamman Ga Sojoji, Ya Ba da Albashinsa Don Tallafi
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wani asusun musamman domin tallafawa sojojin Najeriya, waɗanda suka jikkata a bakin aiki, da kuma iyalan jaruman da suka rasa rayukansu, a wani ɓangare na bikin cikar sa shekaru 74.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, inda ya ce ya umarci Ofishin Babban Akanta na Tarayya da ya buɗe asusun musamman domin wannan shiri.
A cewarsa, an ƙirƙiri asusun ne domin ba da tallafi kai tsaye ga sojojin da suka samu raunuka yayin aiki, da kuma zawarawa, mazajen da matansu suka rasu, da ’ya’yan waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa.
A wani mataki na nuna jajircewa, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa duk albashinsa tun bayan hawansa mulki za a zuba shi cikin wannan asusu a matsayin jari na farko, ba tare da la’akari da wasu tsare-tsaren jin daɗin sojoji da ake da su ba.
Ya jaddada cewa wannan shiri ba sadaka ba ne, illa wani nauyi ne da ya rataya a wuyan ƙasa na girmama da kuma kula da waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu domin zaman lafiya.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnoni, ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ɓangaren masu zaman kansu, da sauran masu hannu da shuni su bada gudummawa domin tallafawa wannan asusu da ƙarfafa gwiwar sojojin da ke fagen daga.
Ana sa ran za a fitar da cikakkun bayanai kan asusun nan gaba kaɗan.
Shugaba Tinubu ya ƙara jaddada cewa bai kamata ƙasa ta manta da irin sadaukarwar da sojoji ke yi ba, tare da iyalansu.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0