Tinubu Ya Amince da Ƙarin Mutane 50,000 Domin Shirin NYSC a 2026
Tinubu Ya Amince da Ƙarin Mutane 50,000 Domin Shirin NYSC a 2026
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙara yawan masu shiga shirin National Youth Service Corps (NYSC) da mutum 50,000 a shekarar 2026 domin rage jinkirin da ake samu wajen tura sabbin masu digiri aikin yi wa ƙasa hidima.
Daraktan Janar na NYSC, Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin bikin kaddamar da asibitin da aka gyara a hedikwatar NYSC, wani bangare na bikin cikar sa shekara guda a ofis.
A cewarsa, ƙarin guraben da shugaban ƙasa ya amince da su na cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, kuma hakan zai taimaka wajen magance matsalar dogon lokaci da masu digiri ke jira kafin a tura su sansanin NYSC.
Nafiu ya ce da wannan sabon mataki, ana sa ran NYSC za ta tura kimanin matasa 418,000 domin yi wa ƙasa hidima a shekarar 2026. Ya bayyana cewa yawan masu kammala jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya ya karu sosai cikin shekaru da dama, lamarin da ya sa ake samun cinkoso wajen mobilization.
Ya kara da cewa a shekarun farko na shirin NYSC a 1973, akwai kasa da cibiyoyin ilimi 12 da ke samar da daliban da za su shiga shirin, kuma a wancan lokaci an tura kimanin mutane 2,364 kacal domin yi wa ƙasa hidima. Amma a yanzu akwai sama da cibiyoyin ilimi 400 da ke fitar da kusan 600,000 masu digiri a kowace shekara.
Sai dai ya bayyana cewa ba duka masu digiri ne ke shiga NYSC ba a kowace shekara, domin wasu na samun takardar keɓewa (exemption), yayin da wasu kwararru kamar likitoci da lauyoyi ke bukatar ƙarin horo kafin su shiga shirin.
Daraktan Janar din ya kuma jaddada cewa tsarin tura matasa aikin hidima yanzu yana amfani da tsarin na’ura mai sarrafa kansa (automated system) domin tabbatar da gaskiya da inganci. Ya ce wasu jinkiri na faruwa ne saboda wasu jami’o’i ba sa lodawa jerin sunayen dalibai a kan lokaci, ko kuma wasu matasa na ƙin zuwa jihohin da aka tura su.
A nasa bangaren, Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ya yaba wa shugabancin NYSC bisa matakan da ake dauka domin inganta jin dadin ma’aikata da masu yi wa ƙasa hidima. Ya kuma gargadi ‘yan hidimar ƙasa da su guji yin tafiya da daddare saboda matsalolin tsaro a wasu yankunan ƙasar.
An kafa shirin NYSC ne a shekarar 1973 domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma bai wa matasa damar yin aiki a jihohin da ba na asalin su ba.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0