WATA KUNGIYA ZATA BADA RABIN KUDIN TIKEKI GA DR. NASIR DON NUNA SOYAYYA A GARESHI.
An yi kira ga Dr. Nasir Ibrahim (Dujiman Ajiyan Gombe) da ya fito takaran kujeran wakilcin Gombe/Kwami/Funakaye a zaben 2027
Daga Umar Shuaibu
Wata babbar kungiyar matasa mai kare muradun al'ummar yankin Gombe ta Arewa (Coalition of Gombe North Youths) ta nemi Dr. Nasir, ya fito takaran kujeran wakilcin Gombe/Kwami/Funakaye a zaben 2027 domin samar da kyakkyawan wakilci nagari a yankin.
Kungiyar ta ce tayi la'akari da cancantar Dr. Nasir da kuma gogewarsa wajen samawa al'umma cigaba ta bagare daban-daban musammam ta fuskar kasuwanci, da kuma duba da irin yadda yake da tausayi da taimakon al'umma a duk inda ya samu wata dama.
A daya bangaren kuma kungiyar ta yi kira ga al'ummar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye da su mara wa Dr. Nasir baya domin samar da wakilci nagari don ci gaban al'ummar yankin gaba daya.
Daga karshe kungiyar sunyi ikirarin bada kaso hamsin cikin dari (50%) na kudin sayan tiketin tsayawa takaran kujeran ga Dr. Nasir idan har ya amince don nunawa duniya nagartan sa.
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0