Shugaban Mulkin Soja na Burkina Faso Ya Soki Dimokuraɗiyya, Ya Nemi Jama’a Su Haƙura Da Ita

Apr 3, 2026 - 15:11
Apr 3, 2026 - 16:58
 0  12
Shugaban Mulkin Soja na Burkina Faso Ya Soki Dimokuraɗiyya, Ya Nemi Jama’a Su Haƙura Da Ita

Shugaban gwamnatin mulkin soja na ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa kamata ya yi jama’a su haƙura da tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa tsarin bai kawo ci gaba face koma baya ga ƙasar.

Traoré, wanda ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a watan Satumban shekarar 2022, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi, inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda dimokuraɗiyya ke tafiya a ƙasashen Afirka, musamman a ƙasarsa.

A cewarsa, tsarin dimokuraɗiyya bai taimaka wajen kawo tsaro, walwala da cigaban tattalin arziki ba, illa ma ƙara dagula lamura da jefa ƙasa cikin matsaloli. Ya ƙara da cewa akwai buƙatar sake duba tsarin shugabanci domin nemo hanyoyin da za su fi dacewa da yanayin ƙasar.

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan makomar mulkin soja a ƙasar, inda wasu ke ganin shugaban na da niyyar tsawaita zamansa kan karagar mulki fiye da yadda aka tsara tun farko.

Tun bayan juyin mulkin da ya kawo shi kan mulki, Traoré ya sha alwashin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, musamman hare-haren masu tayar da ƙayar baya. Sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar ƙalubale a wannan fanni.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa kalaman nasa na iya ƙara janyo muhawara a cikin gida da ma a matakin ƙasa da ƙasa, musamman ma daga masu fafutukar kare dimokuraɗiyya.

A halin yanzu dai, jama’a na jiran ganin irin matakan da gwamnatin mulkin soja za ta ɗauka nan gaba, da kuma ko za a samu dawowar mulkin farar hula a ƙasar kamar yadda aka yi alƙawari a baya.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0